in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun rasu sakamakon fashewar wasu abubuwa a Nairobin Kenya
2014-04-01 10:19:13 cri

Rahotanni daga birnin Nairobin kasar Kenya na cewa, mutane 6 sun rasu, yayin da kuma wasu 10 suka jikkata, sakamakon fashewar wasu abubuwa a yankin Eastleigh dake wajen birnin.

An ce, wasu 'yan ta'adda ne suka jefa wasu ababen fashewa biyu a wasu wuraren marasa nisa da juna, dake cike da jama'a, inda nan take hakan ya haifar da rasuwar fararen hula 6.

Mataimakin kwamandan 'yan sandan lardin Nairobi Moses Ombati ne ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, tuni jami'an tsaro suka isa wajen domin fara gudanar da bincike. Hakan dai na zuwa ne kwana guda, bayan da wani dan ta'adda ya rasa ransa, sakamakon tashin wani abu da yake kokarin hadawa a yankin na Eastleigh.

A baya bayan dai mahukuntan kasar na daukar karin matakan tsaurara tsaro, domin dakile hare-haren 'yan tada kayar baya. Inda ko da a ranar Juma'ar da ta shude, sai da shugaba Uhuru Kenyatta ya gana da al'ummun Somaliya mazauna kasar ta Kenya, da nufin lalubo hanyoyin kawo karshen matsalar tsaron dake addabar kasar.

Don gane da hakan, shugaba Kenyatta ya jaddada kudurin gwamnatin sa, na kawo karshen salwantar rayukan fararen hula, sakamakon hare-haren da ake dangantawa da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida. Ya ce, sashen yawon shakatawa a kasar ya shiga wani mawuyacin hali, sakamakon matsalar ta tsaro, wanda hakan ya sanya kasar asarar kaso 10 bisa dari na mizanin GDP da sashen ke samarwa.

Kenya na shan fama da hare-haren ta'addanci daga magoya bayan kungiyar Al-Shabaab, wadda ke zargin kasar da taimakawa gwamnatin Somaliya wajen fatattakar mayakan ta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China