in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda a Najeriya su shiga farautar 'yan bindigar da suka hallaka mutane a Kaduna
2014-03-17 11:02:19 cri

Rundunar 'yan sanda a Najeriya, ta ce, ta fara farautar wasu 'yan bindiga da suka hallaka akalla mutane 100, yayin wasu hare-hare da suka kaddamar a wasu kauyukan dake kudancin jihar Kaduna.

Maharan su kimmanin 40 da ake zaton Fulani makiyaya ne, sun kaiwa kauyukan hari ne da yammacin ranar Juma'a, da kuma safiyar Asabar. Baya ga mutanen da suka hallaka, sun kuma kone gidaje da dama.

Da yake karin haske kan wannan batu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna Aminu Lawan, ya ce, jami'an tsaro sun shawo kan lamarin, an kuma maido da doka da oda a yankunan da lamarin ya auku. Har ila yau mai magana da yawun 'yan sandan ya ce, ko shakka babu rundunar za ta bankado wadanda suka aikata wannan ta'asa, tare da gurfanar da su gaban kuliya.

A wani ci gaba kuma, fadar gwamnatin jihar ta Kaduna ta fara daukar matakan gudanar da bincike kan wannan lamari. Hakan kuwa ya biyo bayan Allah wadai da gwamnan jihar Mukhtar Yero ya yi da aukuwar hare-haren. Gwamna Yero ya bayyana kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da tsantsar rashin imani. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China