Ofishin MDD a Sudan ta Kudu UNMISS a ranar Litinin din nan 10 ga wata ta bukaci tattaunawa a siyasance da dukkan wakilan siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma mambobin jam'iyar SPLM da aka tsare a kasar domin a cimma wata matsaya ta zaman lafiya.
A karshen makon da ya gabata ne ofishin ya dauki nauyin ziyarar tawagar kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD zuwa Malakal na jihar Upper Nile mai arzikin man fetur dake da tazaran kilomita 600 daga arewacin Juba, babban birnin kasar domin a daidaita game da mallakar wurin kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar zaman lafiya.
A bayanin da kakakin MDD Martins Nesirky ya yi wa manema labarai, ya ce, a safiyar wannan rana, jami'an IGAD din suka ziyarci Bor a jihar Jonglei, UNMISS ya ce, ya tattauna da IGAD a wurare biyu.
Ana dai sa ran wakilan magoya bayan gwamnati da masu adawa da gwamnatin za su hadu a Adis Ababa, babban birnin kasar Habasha a wannan rana ta Litinin.
Bangarorin biyu dai sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan da ya gabata sakamakon tattaunawar sulhu da kungiyar IGAD ta zama mai shiga tsakani.
A wani labarin kuma, ofishin MDD a kasar Sudan ta Kudun tana cigaba da sintiri na jami'an tsaro soja da 'yan sanda a wassu wurare a kasar. A Nassir na jihar Upper Nile, ofishin ta ba da rahoton cewa, yanayin da ake ciki na da rauni, sannan ya samu rahoton fada a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan adawa a Thorgwang a gundumar Manyo. (Fatimah)