in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNMISS ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Sudan ta Kudu
2014-04-22 10:00:12 cri

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu, ta yi kakkausan suka game da kisan daruruwan fararen hula a garin Bentiu cikin makon jiya bisa dalilai na kabilanci.

Wata sanarwa da jagoran ofishin na UNMISS, Raisedon Zenenga ya sanyawa hannu, ta ce, sashen kula da kare hakkokin bil'adama na ofishinsa, ya tabbatar da cewa, yayin da dakarun 'yan adawa suka kwace garin na Bentiu, sun kaddamar da farmaki kan asibitoci, da masallatai, da majami'u, da kuma harabar ofishin shirin abinci na duniya dake yankin.

Sanarwar ta kara da cewa, an kai hare-haren ne a ranekun 15 da 16 ga watan Afirilun nan, bayan da jami'an UNMISS suka killace al'ummun yankunan Bentiu da Rubkona, wadanda ricikin kabilancin kasar ya rutsa da su.

Ya zuwa yanzu dai tawagar wanzar da zaman lafiyar dake kasar ta Sudan ta Kudu, na baiwa sama da mutane 12,000 kariya a sansaninta, baya ga wasu karin mutane 60,000 a wasu sassan kasar daban daban.

Cikin waccan sanarwa, Zenenga ya yi kira ga daukacin sassan da wannan batu ya shafa da su kauracewa rura wutar rikici, su kuma tabbatar da kare rayukan fararen hula yadda ya kamata.

Tun dai a watan Disambar bara ne fada ya barke tsakanin gwamnati da dakarun 'yan adawa kasar, lamarin da ya tilasta mutane akalla 75,000 tserewa sasanonin MDD dake kasar domin tsira da rayukansu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China