Wakilan gwamnatin kasar Mozambique da na 'yan tawayen Renamo, sun bayyana fatan cimma kudurin tsagaita wuta nan da ranar Laraba.
Hakan dai ya biyo bayan zaman da sassan biyu suka gudanar a ranar Litinin, inda suka karbi cikakken rahoton da kwararru ta fuskar aikin soji suka gabatar musu. Rahoton dake kunshe da tsarin da za a bi, wajen samun nasarar shirin shiga tsakani, da tawagar wakilan kasashen ketare za su yi, domin kwance damarar dakarun Renamo.
Da yake karin haske don gane da halin da ake ciki, ministan ma'aikatar noma na kasar Jose Pacheco, wanda kuma ke jagorantar sashen gwamnatin Mozambique, ya ce, muddin tattaunawar ta ci gaba kamar yadda ake fata, batutuwa kadan ne za su rage nan da Laraba, a kokarin da ake yi na kawo karshen ayyukan tada kayar baya, da dakarun Renamon ke aiwatarwa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai sassan biyu, suka amince da kafa tawagar 'yan sa ido, da za ta kunshi wakilan kasashen Botswana, da Zimbabwe, da Kenya da Afirka ta Kudu. Saura za su hada da wakilan Cape Verde, da Italiya, da Portugal, da Amurka da kuma na Birtaniya.
Har wa yau, an amince da kafa babbar rundunar hadin gwiwa mai wakilan kasar 70, da kuma na kasashen waje 23, duka dai da nufin warware matsalar siyasa dake addabar kasar. (Saminu)