A jiya Talata ne aka yi bikin ranar duniya ta bana, bikin da aka kebewa ranar 22 ga watan Afirilun ko wace shekara, domin nazarin halin da doron duniyar nan ke ciki.
Cikin sakonsa game da wannan rana, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga daukacin kasashen duniya, da su kara kaimi wajen wanzar da ci gaba ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta. Ya ce, kamata ya yi al'ummun duniya su zage damtse wajen kaucewa yin abubuwan da ka iya lalata muhalli.
Mr. Ban ya kara da cewa, daukacin albarkatun da bil'adama ke matukar bukatar su, kama daga ruwa, da iska da abinci, suna fuskantar kalubalen gurbata daga ayyukan bil'adama.
An dai yi amfani da wannan rana wajen gabatar da makaloli, da tattaunawa tsakankanin masana kan tasirin ingantaccen muhalli ga rayuwar dan adam.
A shekarar 2009 ne dai babban zaman MDD ya ware ranar 22 ga Afirilun ko wace shekara, domin bikin ranar ta duniya, da nufin samar da daidaito tsakanin bukatun tattalin arziki, da na muhalli da zamantakewar bil'adama a wannan duniya. (Saminu)