in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Angola ya bayyana bukatar dakile ayyukan 'yan tawaye a DRC
2014-03-26 10:12:20 cri

Shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, ya bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta dakatar da abin da ya kira ayyukan bata gari, a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC.

Shugaba Santos, wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin taron shuwagabannin kasashen dake yankin babban tafkin Afirka, ya ce, duk da irin ci gaban da yankin ke samu, a hannu guda akwai tarin matsaloli dake addabar kasar Congo, matakin da ka iya barazana ga zaman lafiya, da tsaron yankin baki daya.

Daga nan sai ya jaddada bukatar daukar matakai daban daban, ciki hadda na soji da na siyasa, domin maido da yanayin zaman lafiya mai dorewa a kasar, yana mai cewa, bai dace a bar al'amura su kara tabarbarewa a yankin ba.

Har wa yau shugaban kasar ta Angola, ya bayyana daukar matakan dinke baraka, da cimma daidaito tsakanin al'ummu daban daban dake yankin, a matsayin muhimman matakan magance matsalolin da ake fuskanta.

Shuwagabannin kasashen jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Ruwanda, da Uganda, na cikin wadanda suka samu halartar wannan taro. Yayin da kuma shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya kasance bako na musamman. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China