in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Mauritaniya za ta kafa wani yankin kasuwanci a Nouadhibou
2012-06-15 11:10:07 cri

Kasar Mauritaniya ta bayyana shirin kafa wani yankin kasuwanci a Nouadhibou, babban birnin tattalin arzikin kasar bisa zummar samar da 'yancin gudanar da musanyar kasuwanci, a cewar wata sanarwar da ta fito bayan taron ministoci a ranar Alhamis.

Taron ministocin ya yi maraba da wannan tsarin doka dake baiwa gwamnatin kasar amincewa da sanya hannu kan kudurin dokar kafa yankin kasuwanci na Nouadhibou, in ji sanarwar.

Yankin Nouadhibou na kunshe da dimbin albarkatun muhalli da na fakewa, haka kuma yanki ne dake tattare da muhimman abubuwa dake ba shi damar kasancewa wani yankin yin musanyar kasuwanci da ma zama cibiyar samun cigaba, in ji ministan tattalin arzikin kasar Sidi Ould Tah a gaban manema labarai.

Haka kuma birni ne dake kusa da nahiyar Turai da Afrika dake bakin ruwan tekun kasa da kasa, bayan wannan kuma Nouadhibou ya kasance wata kofa dake taimakawa duk wasu harkokin kasar Mauritaniya dake nasaba tuno iskan gas da ma'adinai, in ji mista Ould Tah.

Ministan ya kara da cewa, muna fatan kammala wannan aiki na Nouadhibou kafin karshen shekarar 2012.

Birnin Nouadhibou na arewacin kasar Mauritaniya mai tazarar kilomita 450 da Nouakchott, haka ya kasance babban birnin kasuwanci na kasar kuma babbar tashar ruwa wajen fitar da ma'adinai da kifi zuwa yankin Turai da Asiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China