Rahotanni daga Sudan ta Kudu, na cewa, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar UNMISS, ta fara aikin sauyawa dubban al'ummar kasar da yaki ya raba da gidajen su matsugunai, sakamakon saukar damuna. A 'yan kwanakin da suka gabata ne dai wani ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya haddasa ambaliyar ruwa, tare da lalata daruruwan tantunan da UNMISS ta kafawa 'yan gudun hijirar a Juba.
A cewar kakakin MDD Stephane Dujarric, rage cinkoso a sansanonin 'yan gudun hijirar ne babban kalubalen da ake fuskanta yanzu haka. Har ila yau UNMISS na da burin fadada sansanonin dake Malakal, da Bentiu, da Bor da na Juba. Baya ga sabbin wuraren fakewa da ake fatan kafawa a Juba da Bor.
Dujarric ya kara da cewa, tuni al'amura suka fara daidaita a Bor, helkwatar jihar Jonglei dake kudancin kasar, yankin da a baya yaki ya daidaita.
Dauki ba dadin da ya barke tsakanin sojojin gwamnatin kasar da dakarun 'yan adawa a Sudan ta Kudun a tsakiyar watan Disambar bara, ya raba kimanin mutane 706,000 da gidajen su, cikin hadda kimanin mutane 77,000, da yanzu haka ke samun mafaka karkashin kulawar tawagar ta UNMISS. (Saminu)