Babbar hukumar koli ta zaben shugaban kasa a Masar, ta kebe ranar 26 zuwa 27 ga watan Mayu, ya zamanto ranar zaben shugaban kasar, a karon farko, tun bayan da aka ture gwamnatin Islama ta tsohon shugaban kasa, Mohammed Morsi.
Wata sanarwa da ta fito daga babbar kotun kolin zaben kasar ta ce, su kuma, 'yan kasar Masar mazauna kasashen waje, an kebe masu kwanaki hudu, tun daga 15 zuwa 18 ga watan Mayu domin kada kuri'unsu.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewar, daga ranar Litinin ta yau ne, watau 31 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Aprilu, za'a bude kofar yin rajista da kuma zaben, wanda zai tsaya takarar shugaban kasar.
Kamar dai yadda shugaban hukumar koli ta zaben, Anwar al-Assi ya bayyana, za'a iya fara gudanar da kamfe na neman tsayawa takarar zaben shugaban kasa a ranar 3 ga watan Mayu.
A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon ministan tsaro, Field Marshal Abdel-Fattah al-Sisi ya bayyana aniyarsa akan cewar, zai shiga takarar zaben shugaban kasar.
Shi dai tsohon ministan na tsaron ya samu farin jininsa da ya karu, bayan da ya sa hannu a wajen tunkude tsohon shugaban kasar Morsi daga mulki a watan Yulin da ya gabata, a sakamakon wata zanga-zanga da ta gama gari.
Kwararru suna hasashen cewar, shi dai tsohon ministan tsaron ba ya cikin wata barazana ta fuskantar gagarumar adawa a zaben na shugaban kasar, ana kuma sa ran, zai samu nasara ba tare da wata wahala ba.
To amma ba wai tsohon ministan tsaron kawai ba ne ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar zaben shugaban kasar, shi ma shugaban bangaren 'yan mazanjiya Hamdeen Sabahy, shi ma ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasar. (Suwaiba)