A kasar Aljeriya, an bude kamfen zaben shugaban kasa tun ranar Lahadi har zuwa 13 ga watan Afrilu.
'Yan takara shida ne za su fafatawa a zaben wannan karo, daga cikinsu kuma akwai shugaban kasa mai barin gado Abdelaziz Bouteflika.
A yanzu haka masu sanya ido kan al'amuran siyasa sun nuna cewa, za'a goga sosai tsakanin Bouteflika da tsohon faraminista Ali Benflis.
Benflis da ya kasance babban abokin takara na Bouteflika, an nada shi a matsayin faraminista a cikin watan Agustan shekarar 2000 a karkashin shugabancin Abdelaziz Bouteflika, amma ya bar mukaminsa a cikin watan Mayun shekarar 2003 bayan wani sabani tsakaninsa da shugaban kasa.
An zabe shi sakatare janar na jam'iyyar FLN a cikin watan Satumban shekarar 2001 sannan kuma aka sake mai da shi a cikin watan Maris na shekarar 2003.
Daga bisani ya shiga zaben shugaban kasa a shekarar 2004, bayan sanar da sakamakon a ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 2004, ya yi marabus daga jam'iyyar FLN tare da yin allla wadai kan magudin da aka tafka a yayin zabubukan.
Benflis ya janye daga fagen siyasa, sanan ya dawo siyasa bayan shekaru goma a matsayin 'dan takaran zaben shugaban kasa na 17 ga watan Afrilu mai zuwa. (Maman Ada)