Dalilin yajin aiki, bangaren masana'antun kirkiren kasar Afirka ta Kudu ya fadi warwas a cikin watan Satumba da -3,3 cikin 100, idan aka kwatanta da na 0,2 cikin 100 a cikin watan Oktoban da ya gabata, a cewar wasu alkaluman da ake fitar a ranar Litinin.
Wannan shi ne adadin bunkasuwa mafi kankanta da ya janyo fado zuwa -0,6 cikin 100 a fannin sarrafawa, in ji hukumar kididdiga ta Statistics SA a ranar Litinin.
Hukumar ta gabatar da wadannan bayanai a lokacin da dubun dubatar ma'aikata ke gudanar da wani sabon yajin aiki tun yau da kwanaki biyar a jere.
Wannan yin fatali da aiki ya shafi jigilar da motoci zuwa tashoshin ruwa domin fitar da su da kuma kamfanonin da ke kera su na kasar.
A cikin watan Agusta da na Satumba, yajin aiki a kamfanonin kera motoci ya gurgunta wannan sana'a sosai a duk fadin kasar.
Bangaren harhada motoci ne da yajin aiki ya fi ta'azara da ja da baya na kashi 47,3 cikin 100 da 69,9 cikin 100 a cikin watan Agusta da na Satumba, sa'an nan ya biyo kayayyakin harhadawa da makamantansu da -3,3 cikin 100 da -46,0 cikin 100 a daidai wannan lokaci, a cewar hukumar Statistics SA. (Maman Ada)