An yi asarar rayukan akalla mutane 16, a yayin da wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba, suka kaddamar da wani hari ranar Talata, 4 ga wata da dare, a yankin Rim, dake jihar Plateau a tsakiyar arewacin Nigeriya.
Kakakin 'yan sandan jihar ta Plateau, Felicia Anslem ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a birnin Jos na jihar ta Plateau cewar, an kone fiye da gidaje dari biyu, amma ta kaucewa kara bayar da haske a kan lamarin.
Babban birnin jihar ta Plateau Jos ya abka cikin arangamar da ta haifar da zubar da jinin jama'a, a ranar 7 ga watan Maris din shekarar ta 2010 a lokacin da Musulmai da Kiristocin jihar, suka yi karin fargaba da juna a matsayin wata ramuwar gayya ta kisan da suke ganin an yiwa al'umominsu. (Suwaiba)