Shugaba Abdelaziz Bouteflika, ya bayyana rabuwar kan sassan jami'an tsaron kasar, a matsayin wata makarkashiryar da wasu ke yi domin tada zaune tsaye, da burin karya matsayin da kasar ta Aljeriya ke da shi a yankin.
Cikin wata sanarwa da shugaba Bouteflika ya karanta yayin bikin ranar shahidai ta kasar, shugaban ya ce, takun-sakar da ke tsakanin wasu sassan jami'an hukumar sojin kasar, ba abu ne da zai haifarwa kasar da mai ido ba.
Tsokacin na Mr. Bouteflika ya biyo bayan rade-radin da wasu kafofin yada labarun kasar ke yi cewa, akwai rashin jituwa tsakanin babban kwamandan askarawan kasar Janar Gaid Salah, da jagoran sashen tsaron farin kaya Janar Mohamed Mediene Toufik.
Rahotanni dai sun ce, jagororin rundunar tsaron biyu sun raba gari ne, tun bayan da Janar Gaid Salah ya bayyana goyon bayansa, ga takarar shugaba Bouteflika yayin babban zaben kasar dake tafe a watan Afirilu, matakin da Toufik ke matukar adawa da shi.
Don gane da halin da ake ciki, shugaba Bouteflika ya ce, wajibi ne daukacin al'ummar kasar su sanya kishin kasar gaban komai, matakin da a cewarsa, shi zai hana masu burin ganin bayan kasar cimma burinsu. (Saminu)