Hukumomin 'yan sandan Najeriya sun bayar da umurni na tura dimbin jami'an tsaro zuwa jihar Zamfara, domin fafatawa da maharan da ke addabar wasu al'ummar yankin.
Babban sufetan 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar ya bayyana a cikin wata sanarwa, wacce kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, Xinhua ya samu a jiya Litinin cewar, ya ba da umurni na tura wata runduna 'yan sanda ta musamman, wacce ta kunshi rukuni goma na 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma wasu rukuni ukku na 'yan sanda, da kuma rukuni guda na 'yan sandan masu yaki da ta'addanci zuwa jihar ta Zamfara.
Babban Sufetan 'yan sandan na Najeria, ya ba da wannan umurni ne sakamakon wani rahoton halin da harkokin tsaro suke, a yankunan da abin ya shafa, a inda ya ce, ya bayar da umurni na aiwatar da gagarumin ayyukan tabbatar da tsaro daga cibiyar leken asiri ta rundunar sojojin kasar ta Najeriya.
A ranar Asabar din da ta shige ne wasu mahara masu dauke da bindiga, suka abkawa wasu 'yan banga dake gudanar da wani taro a kauyen Unguwar Galadima, wanda ke karamar hukumar Maru, dake arewa maso yammacin jihar ta Zamfara, a inda 'yan bindigar suka kashe fiye da mutane dari. (Suwaiba)