in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Najeriya sun ce sun hallaka 'yan ta'adda 18 a jihar Borno
2014-03-25 09:49:13 cri

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta samu nasarar hallaka mayakan sa kai 18, a ci gaba da simamen da jami'anta ke yi a sassan jihar Borno daban daban.

Cikin wata sanarwa da helkwatar rundunar ta fitar a ranar Litinin, mai magana da yawun ta manjo janar Chris Olukolade, ya ce, sojojin sun harbe 'yan tada kayar bayan ne a Bama da Ngurosoye, dake arewa maso gabashin Maidugurin jihar ta Borno, yayin wani dauki ba dadi a karshen makon da ya gabata.

Olukolade ya kara da cewa, dakarun rundunar sojin sun kuma dakile wasu hare-haren da 'yan ta'addan ke shirya kaddamarwa, tare da kwace makamai da bindigogi da dama. Baya ga wasu tarin motoci da mayakan ke amfani da su, da aka kone kurmus yayin fafatawar.

Ya ce, tuni aka saki wasu mutane 75, bayan da aka tantance su, aka kuma tabbatar ba sa cikin maharan.

Bugu da kari, kakakin rundunar sojin ya ce, kawo yanzu, ba a kai ga tantance sahihancin harin da aka ce an kaiwa wata kasuwa, dake wannan yanki ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China