in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta kaddamar da bikin watan 'yanci na shekarar 2014
2014-04-04 10:43:37 cri

Kasar Afrika ta Kudu ta kaddamar a ranar Alhamis da bikin watan 'yanci na shekarar 2014, tare da yin kira da karfafa kokarin da ake yi domin bunkasa zaman jituwa, gina kasa da sasanta 'yan kasa.

"Shirye-shiryenmu sun shafi tunatar da 'yan Afrika ta Kudu, musammun ma matasa, daga inda muka fito a matsayin kasa, 'yancin walwala muhimmin abu ne da ya zama dole mu nuna kishin kare shi." in ji ministan al'adun kasar Afrika ta Kudu, Paul Mashatile a yayin bikin kaddamar da shirin a birnin Pretoria.

"Muna neman kuma tattara 'yan Afrika ta Kudu, dukkan bangarorin zaman rayuwa domin yin musanyar kwarewarmu ta shekaru ashirin na baya bayan nan, tare da bikin nasarar da muka samu, domin fuskantar kalubaloli da kuma daukar niyyar yin aiki, tare domin samun makoma mai haske da wadata." in ji mista Mashatile.

Bikin kaddamarwa zai gudana nan da 'yan kwanaki masu zuwa daga bakin ranar 27 ga watan Afrilu a yayin da 'yan kasar Afrika ta Kudu suke bikin tunawa da zabubukan farko na kasar bisa tsarin demokaradiyya karo na ashirin.

Mashatile ya ce, "Wannan ya kasance muhimmin matakin farko bisa tarihi wanda ya janyo abin da ake kira al'ajabin Afrika ta Kudu, inda a matsayin mu na kasa, muka samu karfin mantawa tarihinmu mafi muni domin samun makoma mai haske."

Bikin 'yancin walwala da demokaradiyya karo na 20 zai gudana bisa taken "Afrika ta Kudu, wuri mai kyau domin zaman rayuwa". (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China