Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan jerin gwanon motocin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU (AMISOM) da ke kasar Somaliya da kuma dakarun kasar ta Somaliya a wani garin da ke wajen birnin Mogadishu, babban birnin kasar.
Wani jami'in gwamnatin kasar mai suna Mohamed Faraq a yankin Arbiska da ke wajen birnin Mogadishu, wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya tabbatar da cewa, wata mota ce tunkari jerin gwanon motocin da ke tsaye a lokacin, inda ta fada cikin wani rami, sannan ta tarwatse kafin daga bisani sauran motocin su kama da wuta.
Faraq ya ce, mutum guda ya mutu, sannan fararen hula biyu sun ji rauni sanadiyar fashewar da kungiyar mayakan nan ta Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamarwa.
Ko da yake gwamnatin Somaliya da jami'an AMISOM ba su yi wani karin bayani a hukumance ba game da harin da aka kaiwa jerin gwanon motocin, amma a kallon harin a matsayin mayar da martani kan matakan sojan da AMISON ke dauka na fatattakar mayakan Al-Qaida daga maboyarsu a kudanci da kuma tsakiyar Somaliya.
Bayanai na nuna cewa, mayakan sun zafafa hare-harensu ne kan gwamnati da AMISOM a Mogadishu da kuma sauran yankunan kasar. (Ibrahim)