Ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine, ta nuna damuwa game da ziyarar da firaminstan Rasha Dmitry Medvedev ya kai yankin Crimea, ba tare da neman amincewar Ukraine din ba.
Hakan, a cewar kakakin ma'aikatar Eugene Perebiynis, ya sabawa yarjejeniyar kasa da kasa.
A jiya Litinin ne dai Medvedev ya sauka a yankin na Crimea, inda ya gana da jagororin yankin, kan batutuwan da suka jibanci habaka tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ziyarar da ta zo makwanni biyu bayan rattaba hannu kan komawar yankin karkashin ikon kasar Rasha.
Kawo yanzu dai Ukraine ba ta amince da komawar Crimea yankin kasar Rasha ba, tana mai bayyana hakan a matsayin wani mataki na cin iyakar yankin ta. (Saminu)