in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Habasha ya isa Khartoum don tattauna da shugaban Sudan
2013-12-04 09:48:02 cri

A ranar Talatan nan 3 ga wata, firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya isa birnin Khartoum don fara ziyarar aiki ta yini biyu, inda zai tattauna da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.

Kamar yadda kafar yada labaran kasar ta tabbatar, bayan tattaunawa, manyan shugabannin biyu za su rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi na hadin gwiwwa da takardun fahimtar juna da dama wadanda aka riga aka amince da su tun baya a lokacin taron kwamitin ministocin kasashen biyu.

Daga cikin yarjejeniyoyin da za a saka wa hannu tsakanin kasashen biyu, akwai ta ciniki, tattalin arziki, hadin gwiwwar fasaha, da ta bangaren shari'a, sannan da sashen sufurin jiragen sama. Har ila yau, akwai na hadin gwiwwa game da tsarin gwamnati da kuma yarjejeniya game da hidimar da ake samarwa fasinja, tsaro da layin dogo.

Takardun fahimtar juna sun kuma hada da shawo kan fataucin mutane, hadin gwiwwa a bangarorin hada-hadar ajiyar kudade da kwastan da kuma ba da ilimi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China