Babu wasu yankunan da aka gano annobar cutar Ebola a tarayyar Najeriya, in ji gwamnatin wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika, domin kawo karshen jita jitar dake bayyana cewa, an samu bullowar wannan cuta mai haddasa zubar da jini dake kuma kashewa nan take. Amma ana sanya ido a halin yanzu a cikin wasu yankunan wannan kasa, mafi yawan mutane a Afrika, wani nau'in cutar Dengue ita ma da ke haddasa zubar da jini da ake dauka ta hanyar cizon sauro dake dauke da kwayoyinta, in ji sakataren kasa kan harkokin kiwon lafiya mista Khaliru Alhassan a yayin da yake hira tare da 'yan jarida a birnin Abuja. Labaran da ake watsa wa kan bazuwar cutar Ebola a cikin wannan kasa ba su da tushe ko kadan, in ji jami'in. (Maman Ada)