Bisa kididdigar wasannin da ta buga, a cikin watan Oktobar bara ne aka ci kulaf din na Bayern a karon karshe, kafin wannan wasa da Augsburg ta bata ruwa.
Masharhanta kwallon kafa dai na ganin canja 'yan wasa bakwai da kocin Bayern Pep Guardiola yayi ne ya sanya kulaf din na sa, gaza dakile karfin 'yan wasan Augsburg. Ana kuma ganin hakan baya rasa nasaba da yunkurin da kulaf din ke yi na kare matsayin sa a gasar zakarun turai dake daf da kammala.
Yayin wasan dai na ranar Asabar, dan wasan Augsburg Mitchell Weiser ne ya ciwa kulaf din na sa kwallo daya tilo, a minti na 31 da take wasa. Haka kuma aka tashi wannan wasa, Bayern na rike da matsayin ta na daya a teburin gasar ta Bundesliga, yayin da ita ma Augsburg ke ci gaba da kasancewa a matsayin ta na 8.
Ita kuwa Borussia Dortmund dake matsayi na biyu a gasar ta Bundesliga, nasara ta samu kan Wolfsburg da ci 2 da 1. Wannan nasara da Dortmund ta samu ta bata damar kara yiwa kulaf din Schalke nisa da tazarar maki 3, yayin da kuma Wolfsburg ya fada kasa daga matsayi na 5 zuwa na 6.
Yanzu haka dai Bayern Munich ce ke kan gaba a teburin gasar da maki 78, inda kuma Dortmund ke biye. Yayin da kuma Schalke ke matsayi na Uku.(Samiu Alhassan)