A gasar ta Laliga Atletico Madrid ta jefawa Villareal kwallo daya ta hannun dan wasan ta Raul Garcia, aka kuma tashi wasan na ranar Asabar Villareal din na nema. Duk da nasarar da Madrid din ta samu, a hannu guda kulaf din bai nuna cikakken karfin sa ba, sakamakon rashin wasu daga kwararrun 'yan wasansa.
Ita ma Barcelona wadda ta lashe wasanta da Real Betis da ci 3 da 1. Ta buga wasa ne da wasu ke gani sam bai kai ya kawo ba, koda yake bugun daga kai sai mai tsaron gida biyu da Messi ya ciwa kulaf din, da kuma kwallon da Jordi Figueras ya ci gidansu su baiwa kungiyar nasarar da take nema.
Bayan lallasa Real Sociedad da ci 4 da nema, yanzu haka dai Real Madrid za ta fafata ne da Almeria a wasan ta na gaba a ranar Asabar 12 ga watan nan, a matsayin ta na uku a teburin gasar ta Laliga, inda take biyewa Bacelona dake matsayi na biyu, yayin da kuma Atletico Madrid ke ci gaba da kare matsayin ta na daya da maki 79. Bisa hasashe dole ne Real Madrid ta ci wasanta na gaba, muddin ta na fatan kaiwa ga zagaye na gaba a gasar.(Saminu Alhassan)