in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jikkata 'yan sanda 24 yayin rikicin kabilanci a Aljeriya
2014-04-09 10:37:09 cri

Rahotanni daga kasar Aljeriya, na cewa, 'yan sanda 24 sun samu raunuka, an kuma cafke wasu tsagerun matasa su 28, biyowa bayan fadan kabilanci da ya sake barkewa a ranekun Litinin da Talata a Ghardaia.

Dauki ba dadin dai ya auku ne tsakanin kabilar Larabawa ta Chaamba, da kuma ta 'yan kabilar Berber a yankin hamadar Ghardaia, dake makwaftaka da yankunan kasar masu arzikin man fetir.

Tuni dai aka aike da jami'an tsaro yankunan da hargitsin ya auku, domin daukar matakan kwantar da tarzoma, tare da baiwa mutanen da dakarun sa kai ke kewaye da yankunan su kariya.

Wannan dai shi ne fada na baya bayan nan da kabilun biyu suka gwaza, tun bayan dauki ba dadin da suka yi watanni uku da suka gabata. Kawo yanzu, rikicin tsakanin kabilun biyu ya sabbaba mutuwar mutane 13, tare da jikkata wasu da dama. Baya ga gidaje da gonaki da aka kone.

A baya, wannan yanki na hamadar Ghardaia, dake da mutane kimanin 200,000 wuri ne da baki masu yawon shakatawa ke ziyarta, kafin fara aukuwar rikice-rikice tsakanin kabilun biyu da ba sa ga maciji da juna. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China