Ministatan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya gudanar da wata tattaunawa a ranar Talata da takwaransa na kasar Uganda mai ziyara, Sam Kutesa.
Wata sanarwa da aka baiwa manema labarai, ta ce, Wang ya ce, kasar Sin da Uganda za su karfafa huldar gamayya da juna a bangaren samar da ababen more zaman rayuwa, wutar lantarki, arzikin kasa, noma da kuma harkar sadarwa, yawon shakatawa, da bunkasa kwarewar al'umma da sauran bangarori tare da bunkasa manyan ayyuka na hadin gwiwa.
Sanarwar ta ce, ministan harkokin wajen na Sin ya yi kira a kan bangarorin biyu da su kara yawaita musayar ziyara na jama'a da matasa na kasa da kasa da kuma hada kai da kungiyoyi na majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyi wadanda suka kunshi kasashe daban daban.
Sanarwar ta ce, ministan harkokin wajen na Uganda, Sam Kutesa ya nuna jin dadinsa game da tallafin da kasar Sin take baiwa kasar ta Uganda tare da jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su inganta gamayyarsu a bangaren harkokin kasashen ketare domin kare bukatun kasashe masu tasowa.
Ministan harkokin wajen na Uganda wanda ya kawo ziyara a kasar Sin ya yi allah wadai da harin taaddanci da aka kai a birnin Kunming wanda ke kudu maso yammacin kasar Sin a ranar 1 ga watan Maris inda kuma ministan na Uganda ya nuna damuwarsa game da jirgin na kasar Malaysia wanda ya bace watau flight MH370. (Suwaiba)