A sakamakon karuwar tashe-tashen hankula, a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, babban sakataren na majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya furta damuwarsa, tare da tunatar da dukanin masu aikata wannan aika-aika, akan cewa, za su fuskanci shari'a a kan dukanin abin da suka aikata.
A halin da ake ciki, an yi amanna a bisa cewar an hallaka dubannin jama'a, kuma kusan wasu mutane miliyan 2.2 watau kusan rabin jama'ar jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar, na cikin halin bukatar taimakon agaji, a sakamakon barkewar rikicin tun watan Disamban shekara ta 2012, a yayin da 'yan tawayen Seleka, wadanda yawancinsu musulmi ne suka kaddamar da hare-hare.
Hakazalika fiye da mutane dubu 650 ne suka rasa muhallansu, kuma fiye da wasu mutanen dubu 290 ne suka tsere zuwa wasu kasashe dake makwabtaka da jamhuriyar Afrika ta tsakiya domin neman mafaka daga rikicin, wanda ke rikidewa zuwa wani rikici na addini, musamman da mayake kiristoci, wadanda aka fi sani da anti-Balaka sun sami makamai.
A sakamakon wata ziyara da babbar kwamishinar kare hakkin bil'adama, Navi Pillay, ta kai a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya,ta ce, kiyayya tsakanin musulmai da kristocin kasar ta kai wani mataki mai tsanani. A inda kuma kwamishinar ta bukaci kasashen duniya da su kara kaimin agajin taimako zuwa ga wadanda abin ya shafa. A cikin jawabin nasa na jiya Laraba, Ban Ki-moon ya tunatar da duk wadanda ke yin wannan aika-aikar, na yada tashin hankalin, musamman wadanda suke da hannu kai tsaye da kuma masu goyon bayan kungiyoyi masu dauke da makamai a asirce, akan cewa, duk wanda ke da hannu a rikicin, sai ya amsa laifinsa, ta hanyar fuskantar kuliya. Sakatare janar din na majalisar dinkin duniya ya jadadda mahimmanci dake akwai na yin garajen samar da sunayen mutanen da ake ganin suna da hannu wajen tada zane-tsaye, a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, kamar dai yadda kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi kira da a yi, a cikin wani kuduri wanda aka amince da shi a shekarar ta 2013. Kudurin na majalisar ta dinkin duniya ya kuma bayar da umurni na kafa rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya, domin su taimaka a murkushe rikicin kiyaye zaman lafiya. Ban Ki-moon ya kuma nemi a kafa wata hukumar bincike ta duniya, wacce za ta binciki rahotannin na karya hakkin bil'adama daga dukanin bangarorin biyu, tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2013. (Suwaiba)