Manzon musamman na MDD a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, Babacar Gaye ya yi kira a ranar Laraba ga dukkan 'yan Afrika ta Tsakiya da su kawo karshen zubar da jini a cikin kasarsu.
Mista Gaye ya yi wannan kira ne a yayin wani taron manema labarai a Bangui, babban birnin kasar Afrika ta Tsakiya, in ji kakakin MDD, Farhan Haq a gaban 'yan jarida a birnin New York.
A cewar Haq, mista Gaye ya bukaci gungun kungiyoyi masu makamai da su shirya wajen amsa kiran shiga shawarwari tare da hukumomin rikon kwarya.
Haka kuma wakilin na MDD ya yi kira ga hukumomin kasar da su dauki matakai domin fara shirya shawarwarin siyasa bisa manufar gano musabbabin da ya tura kasar cikin wannan kazamin tashin hankali.
Jami'in ya bayyana cewa, tashin hankalin ta fuskar jama'a da tsaro na kara lalacewa, kuma ana kai hare-hare kan gidajen gwamnati da na kungiyoyin kasa da kasa.
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya bukaci a farkon watan Maris da a tura sojojin wanzar da zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya, bayan jerin kiraye kirayen shugabannin kasar na neman taimako domin kawo karshen tashin hankali da kisan kiyashi a cikin wannan kasa.
A cikin wani rahoto zuwa ga mambobin kwamitin tsaro na MDD, mista Ban ya bukaci karin ma'aikatan tabbatar da zaman lafiya domin taimakawa hukumomin Afrika ta Tsakiya maido da tsarin demokaradiya.
Rahoton ya nuna bukatar tura sojoji 10000 da 'yan sanda 1820 ga kasar, aiki na farko na wadannan jami'an tsaro na MDD shi ne kare fararen hula, in ji rahoton na Ban Ki-moon. (Maman Ada)