Kamar yadda gidan radiyon 'Talk Radio 702' a Johannesburg ta yada, a ranar Laraba ne ministan harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Maite Nkoane-Mashabane ya sanar da hakan, ya ce yana da imanin cewa Madam Dlamini-Zuma za ta lashe wannan zaben.
Mambobin kungiyar AU 53 ne za su jefa kuri'a don tabbatar da wannan matsayin a lokacin taronta da za'a yi a Addis Ababa,babban birnin kasar Habasha a karshen watan nan na Janairu.
Gidan rediyon ta ce jami'an kasar Africa ta Kudu suna ta zawarcin sauran mambobi don su goyi bayan Madam Dlamini-Zuma.
Mista Nkoane-Mashabane yace an tsaida shawarar shiga takarar ne a taron kasashe 14 na kungiyar cigaban yankin kasashen kudancin Africa da aka yi a watan Agusta na bara inda Nkosazana Dlamini-Zuma, tsohuwar ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu, ta samu goyon baya gaba daya. (Fatimah)