Bankin duniya ya yi kiran gwamnatocin Afrika da su taimakawa sana'ar yawon bude ido
Bankin duniya ya yi kira a ranar Asabar ga gwamnatocin kasashen Afrika da su dauki dabarun domin bunkasa ci gaban sana'ar yawon bude ido a nahiyar. Bankin duniya ya yi wannan kira a cikin wani rahoto kan ci gaban sana'ar yawon bude ido a nahiyar Afrika da aka fitar a yayin babban taron kungiyar 'yan bude ido ta duniya (OMT) a Livingstone na kasar Zambiya. Yana da muhimmanci na ganin gwamnatocin kasashen Afrika sun shiga baga wajen kirkiro hukumomi da tsare tsare domin tallafawa ci gaban sana'ar yawon bude ido, in ji bankin duniya. Lokaci ya yi ga Afrika da ta bunkasa wannan sana'a matsayin wani ginshikin ci gaba, in ji wannan rahoto.
Wani jami'an bankin duniya, Eneida Fernandes da yake gabatar da rahoton ya nuna cewa mizalin karuwar talauci da rashin ayyukan yi na kwarai a nahiyar suna kasancewa wata dama ga Afrika wajen bunkasa wannan sana'a ta yawon bude ido. A cewar wannan rahoto kuma, gwamnatotcin Afrika ya kamata su fahimci babban matsayin da bangaren sana'ar yawon bude ido na masu zaman kansu, da kafa yanayi mai kyau wajen zuba jari a bangaren masu zaman kansu da kuma samar gine gine ga masu zuba jari. (Maman Ada)