Da yake tabbatar da batun janye yajin aikin ga 'yan jaridu a ranar Jumma'a, kakakin kungiyar ta ma'aikatan sashen hakar ma'adanai ko NUM a takaice Mr. Lesiba Seshoka, ya ce gamayyar kungiyar Injiniyoyin kasar ce ta wakilci kamfanonin hakar ma'adanan, wajen tabbatar da amincewa da bukatar ma'aikatan, matakin da a cewar sa babbar nasara ce gare su.
Seshoka ya ce a yanzu haka an amince da yi wa ma'aikatan karin albashin da ya kai kaso 12 bisa dari, bayan fatali da kungiyar ta NUM ta yi a baya, da tayin kaso 8 zuwa 10 bisa dari daga mahukuntan kamfanonin hakar ma'adanan.
Kimanin ma'aikatan sashen na hakar ma'adanai 90,000 ne dai suka shiga yajin aikin gama gari, tun daga ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata, inda suka bukaci karin albashi, dadi kan albashin wata wata da yawansa ya kai kudin kasar ta Afirka ta kudu Rand 4,000. (Saminu Alhassan)