Babban kwamishinan MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira Antonio Guterres, ya bayyana takaicinsa, game ci gaba da tabarbarewar al'amura a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR.
Guterres wanda a baya bayan nan ya kammala wata ziyarar gani da ido a kasar, ya bayyanawa manema labaru cewa, an ci gaba da dauki ba dadi tsakanin al'ummun kasar, a rikicin da ake dangantawa da banbancin addini da kabilanci.
Ya ce, rikicin wanda dakarun kungiyar Musulmi ta Seleka ta tayar a bara, yanzu haka ya kai ga wani sabon matsayi, inda yake sanadiyar kisan dubban al'ummar kasar. Guterres ya ce, lokaci ya yi da daukacin al'ummar duniya za su dauki matakan da suka wajaba, don shawo kan lamarin, ciki hadda kara yawan jami'an tsaro a kasar.
Tuni dai aka kaddamar da wata kwarya kwaryar gwamnati, da nufin maido da doka da oda, wadda kuma za ta jagoranci babban zaben kasar da ake fatan gudanarwa cikin watan Fabarairun shekara mai zuwa. Sai dai duk da haka a ta bakin babban kwamishinan MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijirar, kawo yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
A wani ci gaban kuma, ofishin shirin samar da abinci na duniya WFP, ya ce, an fara jigilar tan 1,800 na kayayyakin abinci zuwa kasar Afirka ta Tsakiya ta jiragen sama. A wani shirin tallafi da ake fatan zai ba da damar ciyar da al'ummar kasar kimanin 150,000 a tsahon wata guda. (Saminu)