A ranar Laraban nan 12 ga wata, magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da dawowa da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarori biyu dake fada da juna a kasar Sudan ta Kudu, yana mai kira gare su da su bi yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka rattaba hannu a watan jiya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, magatakardan ya jaddada muhimmancin tattaunawar siyasa a kasar baki daya, inda wakilan jam'iyyu da kungiyoyi da suka hada da 'yan jam'iyyar SPLM da aka tsare gaba daya.
Sai dai kuma Mr. Ban ya yi tir da amfani da bama-bamai da aka yi a cikin fadan na Sudan ta Kudu, burbushin da jami'an majalissar karkashin ofishin kiyaye nakiyoyi suka gano a hanyar Juba zuwa Bor dake jihar Jonglei a makon da ya gabata. (Fatimah)