in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu satar mai ne ke janyo malalarsa a Najeriya, in ji kamfanin Shell
2014-03-31 11:05:29 cri

A Najeriya, kamfanin hakar danyan mai na Shell, ya ce, masu satar mai ne ke haddasa kimanin kaso 80 bisa dari, na malalar man a wasu sassan yankin Niger Delta, dake kudu maso kudancin kasar.

Yayin zantawarsa da manema labaru a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa, kakakin kamfanin Joseph Obari, ya ce, yankunan Okordia-Ikarama a jihar ta Bayelsa, na cikin wuraren da aka fi samun wannan matsala ta fasa bututun mai.

Duk dai da hakan, a cewar sa, kamfanin na daukar matakan debe man da ya malala, domin kare yankunan daga gurbatar muhalli. A cewar Obari, daga shekarar 2009 zuwa yau, an samu rahoton kwararar man har karo 21, inda ciki 17 suka auku sakamakon barnata bututun da bata gari suka yi.

Ya ce, a halin da ake ciki, kamfanin na gudanar da aikin kwashe man da ya malala cikin watan Janairun da ya shude, tare da aikin gyaran wuraren da suka gurbata, sakamakon malalar man da ta auku cikin shekarar 2013.

Daga nan sai ya yi kira ga al'ummun yankunan da wannan matsala ta fi kamari, da su kara himmar tallafawa kokarin kamfanin, wajen kare na'urori da kayan aikin sa daga bata gari, duba da irin tallafi da kamfanin ke baiwa al'ummun su, a fagen samar musu da ayyukan yi, da sauran kayayyakin mure rayuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China