Shugaba tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi umarnin baiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yayin jarrabawar daukar aiki a makon jiya guraben aiki yi a hukumar shige-da-ficen kasar.
Fadar shugaban kasar ce ta bayyana hakan, cikin wata sanarwar bayan taron majalissar zartaswar da ya gudana a jiya Labara. Kazalika shugaba Jonathan ya ba da umarnin dakatar da dukkanin wata jarrabawar daukar ma'aikata, wadda ma'aikatu, da hukumomin gwamnati ke shiryawa, in banda ta rundunar soji da 'yan sandan kasar.
A ranar Asabar din karshen makon jiya ne dai masu neman aiki 18 suka rasu a birnin Abuja da wasu jihohin kasar, sakamakon turmutsutsun da ya auku, yayin jarrabawar daukar ma'aikata, ta hukumar shige-da-ficen kasar. Kari kan wasu da dama da suka samu raunuka sanadiyar hakan. Lamari da ya sanya al'ummar kasar bayyana matukar damuwa, kan abin da wasu ke ganin sakaci ne ya jawo shi. (Saminu)