in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da laluben jirgin fasinjan nan na Malesiya da ya bace
2014-03-31 11:03:44 cri

A Litinin din nan ne ake sa ran ci gaba da laluben jirgin fasinjan nan kirar MH370 na kasar Malesiya, wanda ya bace sama da makwanni biyu da suka gabata.

Hakan, a cewar hukumar tsaron gabar ruwan kasar Austireliya AMSA, ya biyo bayan kyautatuwar yanayi a wasu sassan da ake binciken.

Hukumar ta AMSA, ta ce, ana sa ran amfani da jiragen sama 10 a wannan karo, ciki hadda jiragen rundunar sojin saman kasar, da na kasar New Zealand, da na Japanese. Sauran kasashen da jiragensu, za su shiga wannan aiki sun hada da Sin, da Koriya ta Kudu, da Amurka da kuma kasar Malesiya. Baya ga wasu jiragen fararen hula da ake sa ran za su taimaka wajen ayyukan sadarwa.

Har ila yau akwai karin wasu manyan jiragen ruwa 10, na kasashen Sin da Austireliya da za su shiga wannan aiki.

An ce, jirgin ruwan kasar ta Austireliya na dauke da wasu na'urori na musamman, ciki hadda ta gano na'urar nadar bayanan jiragen sama, da aka fi sani da "Black Box". (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China