Wata kotu a kasar Kenya ta ba da belin wasu mutane su 29, da ake zargin kasancewar su masu goyon bayan kungiyar 'yan kaifin kishin Islama ta Al-Shabaab.
Kotun wadda ta ba da belin mutanen kan dalar Amurka 5,800, ta kuma sallami mutane 41 daga cikin su, sakamakon rashin cikakkun shaidun yi musu shari'a. An dai tsafke mutanen ne a birnin Mombasa, makwanni biyu da suka gabata, aka kuma gurfanar da su gaban kuliya a ranar 12 ga watan nan na Fabarairu.
Yayin sauraron karar da aka shigar gaban kotun, lauya mai kare su, ya ce, zargin da ake wa mutanen, na yunkurin shiga kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida ba shi da tushe.
Wannan dai lamari na faruwa ne dai dai gabar da majalissar tsaron kasar ke nuna damuwa, don gane da barazanar samun karuwar masu shiga waccan kungiya, musamman daga wasu masallatai biyu dake Mombasa, da kuma wani guda dake babban birnin kasar Nairobi. (Saminu)