in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bai wa Saliyo dalar Amurka miliyan 30 don aikin gine-gine
2013-02-22 15:03:45 cri

Gwamnatin kasar Sin ta ba da gudummawar kusan dalar Amurka miliyan 30 ga kasar Saliyo don aikin gine-gine na tabbatar da zaman lafiya a kasar dake yankin yammacin Afirka yayin da Jiang Weixin, manzon musamman na shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara ga shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ranar Alhamis din nan.

Jiang wanda har wa yau shi ne ministan gidaje da gine-gine a birane ya isa kasar ne ranar Alhamis da safe don halartar bukin rantsar da shugaba Koroma wanda za'a yi ranar Juma'a.

Cikin jawabinsa ga wasu ministocin kasar da kuma tawagar kasar Sin bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fuskar tattalin arziki da fasaha tsakanin kasashen biyu, shugaban na Saliyo ya ce, wannan gudummawa da kasar Sin ta bayar yana da amfani matuka kuma za su yi cikakken amfani da kudaden wajen kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i wa matasa. da nufin kara bunkasa basira da zammar fasaha wanda ko shakka babu za su yi amfani wajen samar da aiki ga matasa.

Manzon na kasar Sin ya mika sakon taya murna da fatan alheri daga shugabanin kasar Sin tare da bayyana cewa, bisa la'akari da bunkasar tattalin arzikin kasar Saliyo a 'yan shekarun nan, dangantaka dake tsakanin kasar Sin da Saliyo za ta kara kullawa a wasu fannoni.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China