in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yabawa nasarar da Saliyo ta samu wajen warware matsaloli bayan rikicin siyasa
2014-03-06 10:08:48 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yabi kokarin da kasar Saliyo ta yi, a fannin warware matsalolin da kan biyo bayan rikicin siyasa da kasar ta fuskanta a shekarun baya.

Kakakin MDDr Martin Nesirky ne ya rawaito Ban Ki-Moon na bayyana hakan, yayin da ya ziyarci kasar ta Saliyo, domin halartar bikin rufe ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD UNIPSIL a ranar Laraba. Bikin da ya ayyana kawo karshen ayyukan bunkasa sulhu, da tabbatar da daidaito da ofishin ya kwashe shekaru 15 yana aiwatarwa.

Ban wanda ya gana da shugaban kasar ta Saliyo Ernest Bai Koroma yayin ziyara tasa, ya kara da cewa, kasar Saliyo ta koyar da duniya darussa da dama, ciki hadda ikon da al'umma ke da shi na inganta makomarsu. Hakan kuwa ya biyo bayan shafe shekaru 11 da kasar ta yi tana fama da yakin basasa, bayan da 'yan tawaye suka hambarar da gwamnatin shugaba Joseph Momoh.

A watan Nuwambar shekarar 2012 ne dai kasar ta samu nasarar gudanar da babban zaben shugaban kasa, da na yan majalissun dokoki, da kuma majalisun kananan hukumomi, zaben da aka kammala lami lafiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China