Ofishin kare hakkin bil adama na MDD ya yi gargadin tabarbarewar yanayin tsaro a babban birnin jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, sannan yana kokarin ganin a farfado da tsarin shari'a a kasar, kamar yadda kakakin majalissar Martin Nesirky ya bayyana wa manema labarai a wannan rana.
A cewar Mr. Nesirky, ofishin majalissar na babban kwamishina mai kula da kare hakkin bil adama na da rahotannin game da karuwar kisan gilla, karuwar tashe-tashen hankali da miyagun ayyuka a kan titunan birnin Bangui wanda ya zama abin damuwa sosai saboda yanayin wajen gaba daya ya canza.
A cewar ofishin, an kashe wani jami'in gwamnatin wucin gadin kasar a ranar Lahadin nan a kofar gidansa da rana tsaka, gidajen ministocin 'yan kungiyar Seleka da suka hada da tsohon ministan shari'ar kasar, duk an kai musu farmaki aka wawushe su.
Har ila yau, wani ma'aikacin kare hakkin bil adama na majalissar ya aiwatar da wani bincike a Boda, wani dan gari a yammacin Bangui dake nuna cewa, akalla mutane 92 ne aka hallaka a cikin makonni biyu da suka gabata sakamakon harin dake da nasaba da addini.
Ofishin kare hakkin bil adaman na MDD na aiki tare da wassu cibiyoyi domin ganin an farfado da tsarin shari'ar kasar a Bangui. Ofishin kuma ya bukaci a mutunta hakkin dan adama na al'ummar kasar. (Fatimah)