in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na shirin gudanar da bikin cika shekaru 100
2014-02-20 09:51:02 cri

A kalla shugabannin kasashe 28 ne suka bayyana aniyyarsu ta halartar bikin cikar Najeriya shekaru 100 da kasancewa dunkulalliyar kasa.

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Anyim Pius Anyim ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba bayan taron majalisar zartaswar kasar da shugaba Jonathan ya jagoranta, inda ake sa ran shugaban Najeriya zai karbi bakuncin taron kasa da kasa kan zaman lafiya da tsaro a Afirka da zai samu halartar shugabannin kasashen duniya.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, an tsara taken bikin cikar kasar shekaru 100 a matsayin dunkulalliyar kasa ne, ta yadda zai duba muhimman batutuwa da suka shafi hadin kai, bunkasuwa, kasancewar ta dunkulalliyar kasa, da kuma alkawuran da gwamnatin tarayyar kasar ta yiwa al'ummar kasar.

Anyim ya ce, gwamnatin Najeriya ta kafa hukumar amintattu karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Yakubu Gowon, don sarrafa kudaden da za a tara a gidauniyar shirya bikin da za a kaddamar ranar 25 ga watan Fabrairu a Lagos don fara shagulgulan bikin.

Ana fatan taron zaman lafiyan zai janyo hankulan nahiyar Afirka baki daya game da bukatar magance matsalar tsaron da nahiyar ke fuskanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China