in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mozambique za ta shiya zabubuka a ranar 15 ga Oktoban shekarar 2014
2013-11-27 10:18:27 cri

Gwamnatin kasar Mozambique ta ba da sanarwa a ranar Talata cewa, za ta gudanar da zabubuka ranar 15 ga watan Oktoban shekara mai zuwa, wadannan za su kasance zabubuka karo na hudu a kasar tun bayan kazamin yakin basasa da ya kare a shekarar 1992.

David Simango, shugaban jam'iyyar adawar MDM ta kasar Mozambique, kuma magajin garin birnin Beira dake gabar bakin teku, ya bayyana niyyarsa ta aza takararsa a zaben shugaban kasa.

Shugaban kasar mai barin gado, mista Armando Guebuza ya bayyana cewa, zai girmama wa'adinsa na shugabanci kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kuma ba zai nemi sake yin takara ba.

Mista Guebuza, shugaban kasar Mozambique na uku, yana cikin wa'adinsa na biyu na shekaru biyar a matsayin shugaban kasa tun lokacin da aka zabe shi a shekarar 2004.

Jam'iyyar Frelimo, dake kan karagar mulkin kasar tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1975, har yanzu ba ta fitar da 'dan takararta ba a zaben shugaban kasar mai zuwa.

Sai dai kuma babbar jam'iyyar adawar ta kasar, Renamo da jagoranta Afonso Dhlakama sun bayyana niyyarsu cewa, za su kauracewa wannan zabe domin yin watsi da dokar zabe ta yanzu da a cewar take karawa jam'iyyar Frelimo karfi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China