Bayanan da ke fitowa daga Najeriya na bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun kashe mutane 13 a safiyar ranar Alhamis 20 ga wata a kauyen Rapyem da ke gundumar Fan a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato a tsakiyar tarayyar Najeriya.
Kantoman rikon kwarya na karamar hukumar Habila Dung, ya bayyana hare-haren a matsayin "dabbanci kuma abin bakin ciki". Ya ce, an kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, agogon wurin, inda aka halaka mutane 13, ciki har da yara 9, mata biyu da maza biyu, yayin da wasu mutane 5 din da suka jikkata ke samun jinya a asibiti.
Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Felicia Anslem ta tabbatar wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin abkuwar lamarin ta wayar tarho, ko da yake ba ta tabbatar da adadin wadanda lamarin ya shafa ba, amma ta ce, akwai wadanda suka mutu, yayin da wasu mutane da dama suka jikkata.
Yanzu dai an tura jami'an tsaro wurin da lamarin ya faru, don ganin an shawo kan lamarin. (Ibrahim)