Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ya ce, kasarsa na nazartar makomar dangantakarta da Uganda, sakamakon rattaba hannu kan dokar da ta tanaji tsaurara hukunci, ga masu luwadi da madugo, da shugaba Yoweri Museveni na Ugandan ya yi.
Kerry ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa a jiya Litinin. A cewarsa, Amurka na duba yiwuwar gudanar da sauye-sauye a dangantakarta da Uganda, ta yadda daukacin tallafin da take baiwa kasar, zai dace da kudurin kare muradun Amurkan.
Mafiya yawancin tallafin da Amurkan ke baiwa kasar ta Uganda dai sun shafi harkokin kiwon lafiya, da ilimi, da bunkasa ayyukan gona, baya ga shirin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki da Amurkan ta dade tana gudanarwa a kasar.
shugaba Yoweri Museveni na Ugandan dai ya rattaba hannu kan waccan doka, da ta haramta luwadi da madigo ko aure tsakanin jinsi guda ne, bayan da ya ce, binciken masanan kimiyya ya tabbatar da ba a haifar namiji ko mace, da wannan dabi'a ta neman jinsi guda. (Saminu)




