Wani babban jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), kana mataimakin babban sakataren majalisar mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya, Herve Ladsous, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su taimakawa tawagar dake aiki a kasar da kudi da kayan aiki, a kokarin da take yi na kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a kasar.
Ladsous ya yi wannan kiran ne ranar Alhamis, yayin da yake yiwa kwamitin sulhu na majalisar bayani game da yanayin da ake ciki a kasar.
Ya ce, ko da yake al'amura a Bangui, babban birnin kasar sun daidaita, amma har yanzu kungiyoyin da ke dauke da makamai na ci gaba da kashe fararen hula bisa dalilan bambancin addini. Don haka jami'in ya jaddada cewa, muddin ana bukatar a kawo karshen rikicin kasar, to wajibi ne a hada kai tare da daukar matakan da suka dace, ta hanyar tura dakarun wanzar da zaman lafiya da za su mayar da hankali kan kare rayukan fararen hula.
Tun a tsakiyar watan Disamban shekarar 2012 ne, fada ya barke a kasar, lokacin da 'yan tawayen Seleka gabilinsu musulmai suka kaddamar da hare-hare, kana su kuma mayakan anti-Balaka galibi mabiya addinin kirista suka dauki makamai.
A cewar MDD, a halin yanzu sama da mutane 650,000 ne suka rasa gidajensu, kana sama da 290,000 suka tsallaka zuwa kasashen Chadi, kamaru, jamhuriyar demokiradiyar Congo da kuma jamhuriyar Congo. (Ibrahim)