Babbar jami'ar hukumar samar da jin kai ta MDD kana mataimakiyar babban sakataren majalisar mai kula da harkokin jin kai Valerie Amos, ta ce, ta girgiza da abin da ta gani sakamakon tashin hankalin da ya faru a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR, baya ga matsalar tsaro da ake fuskanta.
Madam Amos ta bayyana hakan ne ranar Alhamis ta bakin kakakin MDD Martin Nesirky yayin taron manema labarai da aka kira a Bangui, babban birnin kasar, bayan da ta kammala rangadin da take yi a kasar, inda ta ce, ta kadu matuka da abin da ta gani, ciki har da gidajen da aka kona kurmus, kana jama'a sun firgita da tashin hankali, lamarin da ya tilasta musu kwano a cikin daji.
Yayin rangadin, Amos ta gana da shugabar rikon kwaryar kasar, Madam Catherine Samba-Panza, mambobin gwamnatin rikon kwaryar kasar, shugabannin addinan kirista da na musulunci, wakilan kungiyoyin fararen hula, kungiyoyi da hukomomin jin kai, inda ta shaida musu cewa, akwai bukatar a sasanta, ko da yake har yanzu ba a warware musabbabin tashin hankalin ba.
A makon da ya gabata ne MDD ta kebe karin dala miliyan 10 daga cikin asusunta na agajin gaggawa, don taimakawa ayyukan jin kai na kasar da ke cikin mawuyacin hali. Kuma a cikin watanni 2 masu zuwa ne babban asusun agaji na MDD (CERF) zai samar da kashi na biyu na tallafin.
Bayanai na nuna cewa, kimanin dala miliyan 207 ne masu bayar da agaji suka yi alkawarin baiwa kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin wani taro na musamman da ya gudana a watan da ya gabata a Brussels, inda ya zuwa yanzu aka samar da kashi 30 cikin 100 na kudaden da aka yi alkawarin bayarwa. (Ibrahim)