in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 33 suka mutu a wani sabon hari a arewacin Nigeriya
2014-02-13 12:56:38 cri

Wadansu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a ranar Talatan nan sun hallaka mutane kusan 33 a Konduga dake da nisan kilomita 35 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeriya.

Gwamnan jihar Alhaji Kashim Shettima wanda a Laraban nan ya halarci jana'izar mamatan da suka hada da mazauna kauyen da dalibai 'yan makaranta, ya bayyana wannan ta'asa a matsayin wani rashin imani kuma abin takaici.

Shi ma shugaban karamar hukumar ta Konduga Lawan Gana Ngaleri ya yi bayani cewa, maharan sun je kauyen ne da misalin karfe 4 da rabi na yammacin ranar Talatan cikin jerin gwanon motoci da babura masu suffar kaya na soja, sannan suna sanye da kayayyakin sojoji wanda nan take suka rika jefa ababen fashewa a kusan daukacin gidajen jama'a, abin da ya jawo konewarsu.

Sai dai wani mazaunin garin ya ce, a kalla mutane 53 ne suka mutu, sannan da dama sun bace ba'a gansu ba har yanzu.

Gwaman na Borno ya dai ba da umurni ga kwamishinan kananan hukumomi da a ba da kudi naira miliyan 100 kwatankwacin dalar Amurka 625,000 domin samar da abinci, magunguna, tufafi da barguna ga wadanda harin ya shafa su rage radadin da fargaban da suka shiga.

Ya lura da cewar, kusan kashi 60 zuwa 70 a cikin 100 na gidajen wannan kauye, an kona su kurmus, wadanda suka hada da hukumomin gwamnati da makarantu da kwalejin ilimin kasuwanci da fasahar mulki ta jihar, fadar sarkin garin, shaguna da masallacin Jumm'a. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China