in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya buga waya ga Barack Obama
2014-03-10 14:27:51 cri

A ran 10 ga wata, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya buga waya ga takwaransa na kasar Amurka Barack Obama bisa gayyatar da ya yi masa, inda shugabannin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da halin da ake ciki a kasar Ukraine.

Mista Xi ya bayyana cewa, a shekarar bara, sau biyu ne ya gana da shugaba Obama, inda ra'ayoyinsu ya zo daya a kan wasu manyan batutuwa, tare da daga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, ta yadda za ta dace da sabuwar dangantakar manyan kasashe. Kasar Sin tana son yin kokari tare da Amurka, don tsayawa kan kafa sabuwar dangantaka a tsakaninsu, da girmama gami da kula da babbar moriyar juna da abubuwan da suka mai da hankali a kansu, da kara yin shawarwari, da amincewar juna, da hadin kan juna, ta yadda za a raya dangantakarsu yadda ya kamata. Xi yana sanya ran zantawa da Obama karo mai zuwa, yana mai maraba da uwar gidansa Madam Michelle Obama wadda ke shirya kawo ziyara a Sin a nan ba da dadewa ba.

A nasa bangare, Obama ya yi nuni da cewa, tun da ya gana da Xi a lambun Annenberg har zuwa yanzu, dangantakar da ke tsakanin Amurka da Sin ta samu bunkasuwa. Bana ita ce cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar Amurka da Sin. Amurka tana fatan bangarorin biyu su kara samu sakamako mai kyau daga hadin kansu a wasu manyan batutuwan. Yana san ran zantawa da Xi nan ba da dadewa ba, kuma ya bayyana cewa, uwar gidansa ma na begen ziyarar da za ta kawo a Sin.

Har illa yau, Obama ya jajanta lamarin kasa tumtubar jirgin saman fasinja na Malaysiya, ya ce, Amurka tana son hada kai da Sin a aikin ceton da ake. Bugu da kari kuma, Obama ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamkon lamarin ta'addanci da ya fari a birnin Kunming na Yunan, ya ce, Amurka ta la'anci duk wane irin nau'in ta'addanci, tana son hada kai da Sin wajen yaki da ta'addanci.

Bayan haka kuma, Obama ya gabatar da ra'ayin Amurka kan halin da ake ciki a kasar Ukraine. Xi ya ce, kasar Sin tana rike da matsayinta na adalci da hakikanci kan batun kasar. Halin da ake ciki a Ukraine yana tabarbare, abin mai muhimmanci shi ne, bangarori daban daban da abin ya shafa su yi hakuri, kada su kara tada rikici a Ukraine. Kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan daidaita matsalar ta hanyoyin siyasa da diplomasiyya. Sin tana fatan bangarori daban daban za su yi musanyar ra'ayoyi da samun sulhuntawa, don kawar da bambancin ra'ayoyinsu yadda ya kamata, ta yadda za a ba da taimako wajen warware matsalar Ukraine a siyasance.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China