Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubabkar, ya bayyana matukar takaicinsa, game da kisan dalibai sama da 29, da ake zargin 'yan Boko Haram sun yi a kwalejin ilimi dake Buni Yadi ta jihar Yoben Najeriya.
Atiku ya ce, kisan daliban da ba su ji ba ba su gani ba, wani mummunan aiki ne na rashin tausayi. Daga nan sai ya jajantawa iyalan daliban, tare da kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta zage damtse, wajen ganin ta bullo da sabbin dabarun dakile ayyukan ta'addanci a kasar.
Wannan dai hari na daren ranar Talata, ya zo bayan 'yan awanni, da sanarwar da shugaban tarayyar Najeriyar Goodluck Jonathan ya gabatar, inda ya ce, kofar gwamnatin kasar a bude take, domin tattaunawa da kungiyar ta Boko Haram.
Tuni dai rundunar 'yan sanda da ta sojin kasar suka tabbatar da aukuwar harin. Har ma kakakin rundunar ta soji Eli Lazarus ya bayyana cewa, kawo yanzu ba su tantance yawan daliban da harin ya ritsa da su ba. A hannu guda kuma rundunar 'yan sandan yankin ta ce, maharan sun kone rukunin gidajen malaman kwalejin, tare da lalata turakun sadarwar wayar salula dake garin na Buni-Yadi, wanda ke matsayin hedkwatar karamar hukumar Gujba dake jihar ta Yobe. (Saminu)