Wata majiyar tsaro mai tushe a Najeriya, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, Xinhua cewa, an samu gawawwakin mutane 22 a wani harin da aka kai ranar Alhamis da safe a jihar Filato da ke tsakiyar arewacin kasar.
Majiyar da ta bukaci a sakaye sunanta, ta shaidawa Xinhua cewa, an kidaya gawawwaki 22 da kuma gidaje sama da 10 da maharan suka kona kurmus a Mavo a karamar hukumar Wase dake kudancin jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Chris Olakep, ya tabbatar da abkuwar lamarin, amma ya ki ya bayyana adadin wadanda suka jikkata. Wakilin Xinhua a jihar, ya ce, lamarin ya haifar da zaman dar-dar a karamar hukumar ta Wase, yayin da matasa a yankin suka shiga yin fashe-fashe don nuna rashin amincewarsu da kashe-kashen da suka faru.
Kisan na Wase dai ya zo ne kasa da sa'o'i 48, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai wa wasu al'ummomi hari a yankin Riyom da ke jihar ta Filato, inda suka kashe sama da mutane 20.
Jihar Filato dake tsakiyar Najeriya, ta shafe shekaru tana fama da fadan kabilanci. (Ibrahim)