in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a raya dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha zuwa wani sabon matsayi
2013-03-15 11:17:48 cri

A ranar 14 ga wata da yamma, bisa goron gayyata da aka ba shi, shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho.

Putin ya taya Mr. Xi murna bisa zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Sin, tare da fatan Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa, tare da kawo alheri ga jama'a. Ya ce, dangantakar da ke tsakanin Rasha da Sin ta zama wani muhimmin jigo wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a duniya, kuma tana da ma'ana ta musamman. Yanzu, a cewarsa, Rasha na kokarin shirya ziyarar da shugaban Xi zai kai kasar, yana fatan wannan ziyara za ta inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da yin mu'amalar ayyukan al'adu tsakanin al'umma, tare da karfafa dangantakar bangarorin biyu.

A nasa bangaren, shugaba Xi ya nuna godiya ga Putin, inda ya ce, shugaba Putin ne ya fara buga masa waya don taya shi murnar zama shugaban kasar Sin a lokaci na farko, abin da ya nuna cewa, Mr. Putin ya dora muhimmanci sosai game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha, da irin dankon zumunci da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu. Mr. Xi ya ce, shi zai mai da hankali sosai game da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha, kuma zai dauke shi da muhimmanci cikin manufar diplomasiyya ta kasar Sin.

Xi Jinping ya yi bayanin cewa, yana sa ran yin shawarwari da Mr. Putin yayin ziyararsa a kasar Rasha, kuma za su yi musayar ra'ayi game da inganta hadin gwiwa, da tattauna muhimman batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China